Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kashe sama da yuan biliyan 8.6 wajen tallafawa mabukata
2019-07-29 15:25:43        cri

Gwamnatin kasar Sin ta kashe kudin Sin RMB yuan biliyan 8.61 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.25 wajen tallafawa mutane masu fama da wahalhalu ya zuwa karshen watan Maris na shekarar 2019, ma'aikatar kula da walwalar jama'ar kasar Sin MCA, ta sanar da hakan a yau Litinin.

Sama da mutane miliyan 4.78 ne suke fama da matsin rayuwa a sassan kasar, wadanda suka hada da tsofaffi, da masu bukatar musamman, da kuma kananan yara wadanda ba za su iya yin wata tartibiyar sana'a ba, kuma ba su da takamammiyar hanyar samun kudin shiga, sannan babu wanda ke daukar nauyin bukatun rayuwarsu.

Daga cikin mabukatan, kusan mutane miliyan 4.5 sun fito ne daga yankunan karkara, yayin da ragowar mutane 286,000 daga yankunan birane, kamar yadda Jia Weizhou, kakakin ma'aikatar MCA, ya bayyana a taron manema labarai.

Haka zalika, kusan yuan biliyan 62.77 aka kebe domin biyan kudaden alawus ga mutane miliyan 44 ya zuwa karshen watan Mayun shekarar 2019, kana daga cikin adadin mutane miliyan 9.4 sun fito ne daga yankunan birane. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China