Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin na neman damammakin yin cinikayya da zuba jari a Masar
2019-07-29 09:14:38        cri

Shugaban hukumar bunkasa alakar kasashe masu tasowa ta kasar Sin (CPSSC) Lyu Xinhua ya bayyana kudirin hukumarsa na kokarin cin gajiyar damammaki na yin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari da ma bude hanyoyi na tattauna tsakanin kamfanonin kasashen Sin da Masar.

Da yake karin haske yayin taron dandalin kasuwanci tsakanin Sin da Masar da ya gudana a birnin Alkahiran Masar, Lyu wanda har ila shi ne jagoran tawagar 'yan kasuwan kasar Sin a taron, ya zayyana irin muhimmiyar rawar da kanana da matsakaitan kamfanonin kasar Sin suka taka a jarin da Sin ke zubawa.

Ya ce, wadannan kamfanoni sun samar da kayayyaki masu inganci a kan farashi mai araha, sun kuma biya bukatun kasuwar kasar Masar baya ga fitar da kayayyakin zuwa sauran kasuwanni.

A nasa bangare, jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang, ya bayyana cewa, manufar ziyarar tawagar hukumar ta CPSSC a kasar Masar a halin yanzu, ita ce karfafa alaka tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, dandalin 'yan kasuwar Sin da Masar ya samar da muhimmiyar dama da za ta kai ga cimma wannan manufa.

Jakada Liao ya ce, a halin yanzu duniya na fuskantar sauye-sauye, yayin da Masar da Sin da sauran kasashen Afirka suke shiga wani sabon mataki na ci gaba, inda dukkansu suka shiga shawarar Ziri daya da Hanya daya da kasar Sin ta gabatar.

A yayin taron dandalin na birnin Alkahira, kimanin kamfanonin kasar Sin 19 da 20 daga Masar da suka shafi fannonin ilimi, da raya kasa da tattalin arziki da masana'antu ne suka ci gajiyar alakar cin moriyar juna. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China