![]() |
|
2019-07-27 16:03:30 cri |
A cikin wasikar, shugaba Xi ya nuna cewa, duniya daya tilo Bil Adama ke da ita, hana yaduwar hamada wani babban aiki ne ga bunkasar Bil Adama mai dorewa. Ya ce ya kamata, al'ummar duniya su kara hada kai ta fuskar hana yaduwar hamada da daidaita illar da hamada ke kawowa, da ingiza aikin kiyaye muhallin halittu, kana da tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa kafin shekarar 2030, ta yadda jama'ar duniya za su ci gajiyar muhalli mai kyau.
Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin na ba da muhimmanci sosai kan kiyaye muhalli, kuma tana samun ci gaba mai armashi wajen hana yaduwar hamada. Ya ce yadda ake daidaita hamadar Kubuqi ta kasar Sin, ya zama wata fasahar kasar Sin da za a iya koyi da ita a aikin daidaita muhallin al'ummar duniya da kuma tabbatar da ajandar ci gaba mai dorewa baki daya. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China