Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron baje kolin kayayyakin da ake shiga da fitar da su daga kasar Sin karo na biyu zai samu karin mahalarta
2019-07-26 15:52:12        cri

Taron baje kolin kayayyakin dake shiga da fita daga kasar Sin CIIE karo na 2, da za a yi a Shanghai tsakanin ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, zai samu karin mahalarta fiye da bara.

Yayin wani taron manema labarai da aka yi a yau Jumma'a, kwanaki 100 gabanin taron, mataimakin Ministan kasuwancin kasar Sin Wang Bingnan, ya bayyana cewa, kawo yanzu, kamfanoni sama da 3,000 daga kasashe da yankuna 150 ne suka tabbatar da za su halarci taron .

Wang Bingnan, ya ce kamfanonin sun fito ne daga kasashe mambobin kungiyar G20 da ta BRICS da kungiyar hadin kan Shanghai, tare kuma da kasashe 60 dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasashe 40 marasa karfin tattalin arziki a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China