![]() |
|
2019-07-29 10:26:17 cri |
Wakilin musamman na kungiyar tarayyar Afrika a Sudan ya sanar a jiya Lahadi cewa, a ranar 30 ga watan Yuli ake sa rana za'a sake dawowa kan teburin sulhu don tattaunawa tsakanin majalisar sojoji mai mulkin rikon kwaryar kasar Sudan (TMC), da gamayyar 'yan adawar Freedom and Change Alliance na kasar.
Wakilan bangarorin biyu na TMC, da gamayyar 'yan adawar, an gayyace su da su koma kan teburin sulhu don tattaunawa a ranar 30 ga watan Yuli a Khartoum, babban birnin kasar, domin kammala amincewa da kundin tsarin mulkin kasar da wasu sauran batutuwa, ofishin wakilin musamman na AU ne ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi.
Kundin tsarin mulkin kasar wanda ake sa ran ayyanawa, za'a tattauna kansa tsakanin TMC da gamayyar 'yan adawar, batutuwan da ya kunsa sun hada da tsarin shugabancin kasar da mukamin firaminista wanda ake tunanin kafawa a cikin wa'adin rikon kwaryar kasar.
A ranar 17 ga watan Yuli ne, majalisar sojojin ta TMC da gamayyar 'yan adawar, suka rattaba hannu kan ayyana dokokin siyasar kasar, wanda shi ne zai shata tsarin wa'adin mika mulki a kasar. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China