Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An jinkirta tattaunawa tsakanin majalisar sojojin Sudan da 'yan adawa
2019-07-19 09:56:14        cri
An dage tattaunawar da aka shirya yi a yau Juma'a, tsakanin majalisar sojojin ta rikon kwarya a Sudan (TMC) da 'yan adawar Freedom and Change Alliance na kasar, bangaren 'yan adawar ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis.

Wani kusa a kungiyar 'yan adawar, Munzir Abul-Mali ya ce, an amince da jinkirta taron tattaunawar ne sakamakon rashin cimma matsayar amincewa da kundin tsarin mulkin kasar, sai dai babban jami'in 'yan adawar bai bayyana cikakkun dalilan da suka sanya aka jinkirta gudanar da taron ba.

A ranar Laraba ne, TMC da Alliance, sun sanya hannu a karon farko game da warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, matakin da ake ganin tamkar daura danba ne wajen cimma matsaya domin shirya cikakken tsarin wa'adin mika mulki a kasar.

To sai dai kuma, bangarorin biyu sun amince a dage lokacin rattaba hannu na amincewa da kundin tsarin mulkin kasar, wanda shi ne zai bayyana takamamman wa'adin da gwamnatin rikon kwaryar kasar za ta shafe gabanin mika mulkin.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne wadda aka cimma matsaya kanta karkashin masu shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afrika da gwamnatin kasar Habasha.

Yarjejeniyar ta tanadi a kafa tsarin shugabanci na hadin gwiwa mai mambobi 11, wanda ya hada da fararen hula 5 da wakilan sojoji 5, yayin da za'a zabo mutum guda ta hanyar tuntubar juna tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China