Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin soja na Sudan da masu adawa sun kulla yarjejeniyar kafa hukumar kula da kasa ta wucin gadi
2019-07-18 09:17:02        cri
Kwamitin soja na wucin gadi na kasar Sudan da babbar kungiyar adawa ta kasar FCA, sun kulla wata yarjejeniyar kafa hukumar kula da kasa ta wucin gadi a Khartoum, hedkwatar kasar, a jiya Laraba.

Bisa yarjejeniyar, bangarorin 2 za su hada kai wajen kafa wata hukuma mai kula da aikin mulki cikin wani wa'adin da aka tanada, inda za su girmama juna, da neman daidaita sabaninsu ta hanyar tattaunawa.

An ce, za a kafa wata majalisar mulkin kai ta hadin gwiwa mai kunshe da mutane 11, wadda za ta zama hukuma mai iko na koli. Cikin wadannan mutane 11, akwai fararen hula 6, da hafsoshi 5, yayin da daya daga cikin fararen hulan 6 sai sojojin kasar da 'yan adawa sun tattauna kan wanda zai rike mukamin.

Ban da haka, an kayyade cewa, cikin wasu watanni 21 bayan kulla yarjejeniyar, wani mamba hafsan soji ne zai jagoranci majalisar mulki. Sa'an nan a cikin wasu watanni 18 da za su biyo baya, za a ba wani mamba farar hula damar jagorantar majalisar.

Har ila yau, an kayyade cikin yarjejeniyar cewa, bangarorin kasar za su kafa majalisar ministoci cikin hadin kai, kuma za a ba kungiyar FCA ikon gabatar da sunan wanda zai zama firaministan kasar na wucin gadi.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China