Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Sudan ta sanar da gano yunkurin juyin mulki a kasar
2019-07-25 13:22:25        cri

Rundunar sojin kasar Sudan ta sanar da gano yunkurin juyin mulki, karkashin babban hafsan soji da manyan jami'a na hukumar tabbatar da tsaro da tattara bayanan sirri NISS.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na SUNA na kasar, ya ruwaito sanarwar da rundunar sojin Sudan ta fitar dake cewa, babban kwamandan hadin gwiwar askarawa, Hashim Abdel-Muttallab Ahmed, tare da wasu manyan jami'ai na hukumar NISS da na kungiyar 'yan uwa musulmi da na tsohuwar jam'iyyar NCP mai mulki na da hannu a yunkurin juyin mulkin.

Rahoton ya ce an tsare wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulkin, inda yanzu haka ake gudanar da bincike kafin gabatar da su a gaban kotu.

Rundunar sojin ta ce yunkurin na da nufin hana juyin juya halin kasar, domin dawo da mulkin NCP da yin zagon kasa ga maslahar siyasa da kafa gwamnatin farar hula. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China