Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin mulkin soji da bangaren adawa na gab da cimma yarjejeniya kan mulkin rikon kwarya na hadin gwiwa a Sudan
2019-07-13 16:49:11        cri
Kwamitin mulkin soji na kasar Sudan da kungiyar kawance dake rajin samar da 'yanci da sauyi a kasar, sun amince da yarjejeniyar da za ta tantance jagororin gwamnatin rikon, wanda ya kai su ga dab da sanya hannu kanta a hukumance.

Wakilin Tarayyar Afrika a Sudan, Mohamed Hacen Lebatt, ya ce bangarorin biyu sun gudanar da zagaye na 3 na tattaunawa karkashin kyakkyawan yanayi, kuma dukkansu sun amince da kunshin daftarin yarjejeniyar.

Bangarorin biyu sun kuma amince su gana a yau Aasbar, domin amincewa da daftari na 2, wanda ke kunshe da kundin tsarin mulki.

Wakilin Habasha Mahmud Dirir, ya shaidawa manema labarai cewa, abun da ya rage yanzu shi ne bayyana cimma yarjejeniyar a hukumance, wanda zai alamta shiga wa'adin mulkin rikon kwarya ko kuma sauyawar gwamnati zuwa ta farar hula. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China