Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan:An sake jinkirta tattaunawa tsakanin kwamitin mulkin soji da bangaren adawa
2019-07-15 10:13:03        cri
An sake dage tattaunawar da aka shirya yi jiya Lahadi, tsakanin kwamitin mulkin soji da kungiyar kawance dake rajin samar da 'yanci da sauyi a kasar Sudan.

An gaza gudanar da taron ne a karo na 2 saboda wakilan bangaren adawa ba su hallara ba.

Sai dai kwamitin mulkin sojin ko Tarayyar Afrika, ba su fitar da wata sanarwa dangane da dage tattaunawar ba.

Amma, Khalid Omer Yousif, jagora a kungiyar kawancen 'yan adawar, ya shaidawa manema labarai cewa, kungiyar ta nemi Tarayyar Afrika, daya daga cikin masu shiga tsakanin kan rikicin na Sudan, da ta jinkirta tattaunawar zuwa gobe Talata.

Tattaunawar da ake ta jinkirtawa na da nufin amincewa da kundin tsarin mulki wanda zai ba da iko ga masu mulkin rikon kwarya.

A ranar 5 ga watan nan ne kwamitin sojin da bangaren adawar, suka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi bangarorin biyu.

Bangarorin biyu sun amince da kafa majalisar mulki ta hanyar karba-karba a tsakaninsu na tsawon shekaru 3 da kuma gwamnatin farar hula mai cin gashin kanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China