Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR ta bukaci Sudan ta kudu da ta kawo karshen matsalar raba mutane da muhallansu
2019-07-09 20:25:25        cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) ta yi kira ga jagororin kasar Sudan ta kudu, da su kara zage damtse wajen kawo karshen matsalar raba mutane da muhallansu da ta fi girma a nahiyar Afirka.

Hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar, yayin murnar cika shekaru 8 da kasar ta samu 'yancin kanta, inda ta zama jaririyar kasa a duniya cewa, an samu ci gaba, amma har yanzu ba a samu zaman lafiya ba, sannan ba a kai ga warware wasu muhimman batutuwa ba.

Hukumar ta MDD da abokan huldarta, sun kaddamar da gidauniyar dala biliyan 1.4 don samar da tallafin jin kai ga 'yan gudun hijira. Sai dai kaso 21 cikin 100 na kudaden da ake nema kawai aka tara, yayin da bukatun 'yan gudun hijirar suka dara kudaden dake hannu.(Ibrahim´╝ë

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China