Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sanar da kakabawa Ayatollah Sayyed Ali Khamenei takunkumi
2019-06-25 13:35:32        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sa hannu kan wani umarni a fadarsa, jiya Litinin, inda ya kakaba takunkumi kan Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, jagoran addini na kasar Iran, da hukumomin dake karkashin jagorancinsa.

A cewar Trump, takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran a wannan karo, martani ne ga matakan da Iran ta dauka a jere cikin kwanakin baya, ciki hadda kai hari kan jirgin sama maras matuki na Amurka. A ganinsa, ya kamata Khamenei ya dauki alhakin aiwatar da wadannan matakai na nuna kiyayya. Takunkumin a wannan karo, ya kunshi katse hanyoyin kudin shiga ga Khamenei da ofishinsa da sauran jami'ai masu ruwa da tsaki.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, kasar za ta ci gaba da matsawa Iran lamba ta fannonin siyasa da tattalin arziki, har sai Iran ta yarda da yin shawarwari kan wata sabuwar yarjejeniya.

An kuma ba da labari cewa, a gun wani taron manema labarai da aka yi a wannan rana a Tehran, fadar mulkin Iran, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Ayyed Abbas Al Mousawi ya ce, Iran ba za ta ba da muhimmanci ga tukunkuman da Amurka ta kakaba mata ba ko kadan, domin a ganinta, farfaganda ce kawai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China