Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya nuna damuwa kan yadda Iran ta tace fiye da adadin Uranimun da aka amince
2019-07-02 14:49:41        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna damuwa, game da rahotannin dake cewa, Kasar Iran ta tace fiye da adadin makamashin Uramium din da aka amince mata.

Mai magana da yawun Guterres, Stephane Dujarric ya bayyana cewa, babban sakataren MDD yana sane da rahotanni dake cewa, da alamun Jamhuriyar musulunci ta kasar Iran ta karya yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma ta JCPOA game da adadin makamashin Uranium da za ta iya tacewa.

Dujarric ya ce, idan har wannan rahoto ya tabbata gaskiya, matakin na Iran zai iya kaiwa ga rushewar yarjejeniyar, kuma hakan zai yi illa ga moriyar tattalin arzikin Iraniyawa. Wannan batu kamar sauran batutuwan da suka shafi aiwatar da shirin yana da muhimmanci, kuma ya kamata a warware shi ta hanyar matakan dake kunshe cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar ta JCPOA。

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA, ya ruwaito ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif a ranar Litinin na cewa, Iran ta tace adadin makamashin Uranium da ya zarce Kilogram 300.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China