Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya bukaci da a kara azama wajen aiwatar da matakan inganta rayuwar Sinawa
2019-07-26 11:15:40        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci sassa masu ruwa da tsaki, da su kara zage damtse, wajen aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba na inganta lafiya da rayuwar Sinawa.

Li, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, ya yi wannan kira ne cikin wata takardar umarni da ya aike ga taron masu ruwa da tsaki da ya gudana ta kafafen bidiyo da wayar tarho, jiya Alhamis a nan birnin Beijing.

Cikin sakon nasa, firaminista Li ya jinjinawa sauye-sauye da aka samu a fannin kula da lafiya, da yaki da cututtuka, da inganta lafiyar al'ummar Sinawa musamman a 'yan shekarun baya-bayan nan. Don haka Mr. Li ya sake yin kira da a ci gaba da aiwatar da kudurorin da aka zartas, da tsare-tsaren da aka tanada karkashin shugabancin JKS, da majalissar gudanarwar kasar.

A daya bangaren kuma, firaministan ya yi kira da a dora muhimmanci ga batun kandagarkin cututtuka, a kuma aiwatar da matakai bi da bi, ta yadda nasarar da ake samu a fannin za ta ci gaba da dorewa. Bugu da kari a cewarsa, ya kamata a karfafi gwiwar iyalai da daidaikun al'ummar kasar, ta yadda za su rika daukar matakan da suka wajaba na kula da lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China