Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya jaddada muhimmancin aiwatar da gyare-gyare da bude kofa wajen farfado da arewa maso gabashin kasar
2019-07-02 10:48:54        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa, muhimmin mataki ne na farfado da arewa maso gabashin kasar.

Li Keqiang wanda mamba ne na kwamitin gudanarwa na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya ta JKS, ya bayyana haka ne jiya, yayin rangadin da ya kai Dalian, birnin dake gabar teku a lardin Liaoning na yankin arewa maso gabashin kasar.

Ya ce ya kamata lardin ya yi amfani da rawar da kasuwa ke takawa wajen rarraba albarkatu yayin karfafa matakan sa ido na gwamnati, yana mai kira da aka kara kokarin inganta muhallin kasuwaci ta hanyar rage dokoki masu tsauri da inganta hidimomi.

Da yake jinjinawa yanayin shimfidar lardin Liaoning wajen bude kofa, Li Keqiang ya ce ya kamata a yi amfani da shi wajen zurfafa hadin gwiwa a ciki da wajen lardin da kuma jagorantar farfado da yankin arewa maso gabashin kasar.

A ziyarar da ya kai cibiyar kirkire-kirkire ta kera manyan kayayyaki, Firaministan ya jaddada muhimmancin kirkire-kirkire wajen farfado da arewa maso gabashin kasar Sin, yana mai karfafawa masana kimiyya masu bincike gwiwar samar da kayayyakin da za su karbu a kasuwa da kuma ingiza daukaka bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China