Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya tattauna da wakilai mahalarta taron dandalin Davos na lokacin zafi na shekarar 2019
2019-07-03 20:11:39        cri

Jiya Talata 2 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tattauna da wakilai fiye da 200, wadanda suka halarci taron dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi na shekarar 2019 a birnin Dalian da ke arewacin kasar Sin.

A yayin taron, firaministan Sin ya ce, kasarsa na himmatuwa, wajen kyautata muhallin kasuwancin kasa da kasa da ake iya yin hasashe a kansa, inda za a tafiyar da harkoki bisa ka'idojin kasuwanci, da dokoki ba tare da rufa-rufa ba, kuma za a kara samun tabbaci. Kana kuma kasar Sin za ta takaita jerin sana'o'i, da ayyukan da aka haramta zuba jarin waje a cikin su, sa'an nan za ta kara bude kofarta ga ketare bisa ka'idar "in ba a haramta ba, a ba da iznin shiga".

Har ila yau, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan kiyaye halaltattun hakkokin baki 'yan kasuwa, za kuma a kawar da bambanci tsakaninsu da masu jarin kasar Sin, muddin sun yi rajista a nan kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China