Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin kara azama wajen aiwatar da manufofin bude kofa da sauye sauye
2019-07-24 10:11:47        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a kara azama wajen aiwatar da manufofin bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, domin ingiza ci gaba da kara kyautata rayuwar al'umma.

Firaministan na Sin, wanda kuma mamba ne a zaunannen kwamiti na hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar yini biyu da ya kai yankin gwani na cinikayya maras shinge dake birnin Shanghai.

Yayin wannan ziyara ta ranekun Litinin da Talata, Mr. Li ya ganewa idanun sa yadda kamfanonin cikin gida da na kasashen ketare ke cudanya da juna a yankin cinikayyar maras shinge.

Li Keqiang ya yi kira da a aiwatar da matakan inganta amfani da albarkatun kasuwa da na yankunan gudanar da hada hada, ta yadda yankin zai zamo sansani ga harkokin cinikayya mafiya inganci.

Kaza lika firaministan ya ziyarci kamfanin kayan laturoni na Shanghai, wanda daya ne daga kamfanonin da suka yi fice a sarrafa kayan lantaki, inda ya ja hankalin mahukuntan sa da su shiga takara a kasuwannin duniya, tare da bunkasa karfin kasar a fannin samar da muhimman kayayyakin bukata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China