Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya jaddada kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga kowa
2019-07-01 19:47:56        cri

Da safiyar yau Litinin ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya wato WEF wato Mr. Klaus Schwab, a birnin Dalian na kasar Sin.

A yayin ganawarsu, Li Keqiang ya ce, kasar Sin na son zurfafa huldar abokantaka a tsakaninta da WEF, da fadada hadin gwiwarsu a fannoni daban daban. Kaza lika Sin na fatan hada kai da WEF, wajen yin amfani da damar da sabon juyin juya hali ta fuskar masana'antu ya kawo, don ci gaba da kyautata matsayin taron dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi, a kokarin samar da sabon dandali ga sabbin jagogori na duniya, da kiyaye ra'ayin cudanyar sassa daban daban na duniya, da yin ciniki cikin 'yanci, da kuma tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga kowa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China