Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaba mai jiran gado na babban taron MDD karo na 74
2019-07-04 20:22:47        cri

Yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da Tijjani Muhammad-Bande, shugaba mai jiran gado na babban taron MDD karo na 74.

A yayin ganawar ta su, Li Keqiang ya ce, a matsayinta na daya daga kasashen da suka kafa MDD, mai kuma kujerar din din din a kwamitin sulhu, kana kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan kiyaye tsarin kasa da kasa, wamda ke mayar da MDD gaba da kome, za ta kuma hada kai da kasashen duniya bisa kundin tsarin MDD, wajen zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa, da kiyaye adalci a duniya, da daidaita kalubale tare, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama.

A nasa bangaren, Tijjani Muhammad-Bande ya ce, a matsayinsa na shugaban babban taron MDD mai jiran gado, zai tsaya kan ra'ayin cudanyan sassa daban daban na duniya, da kiyaye kundin tsarin MDD, tare da goyon bayan mambobin MDD su warware matsaloli ta hanyar tattaunawa. Har ila yau zai gudanar da ayyukansa bisa sanin ya kamata, kuma cikin adalci, tare da inganta tuntubar kasar Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China