Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaminsitan kasar Sin ya jaddada muhimmancin bunkasa sana'o'i da kirkire-kirkire
2019-06-14 12:53:35        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a kara bunkasa sana'o'i da kirkire-kirkire domin daidaita samar da aikin yi da bunkasa kirkire-kirkire da karfafa sabon karfin ci gaba.

Li Keqiang ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake bayani game da kokarin gwamnati na inganta bunkasa sana'o'i da kirkire-kirkire, yayin wani taro da ya gudana a Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang dake gabashin kasar.

Da yake bayyana bunkasa sana'o'i da kirkire kirkire a matsayin muhimman ginshikan juriyar tattalin arzikin kasar Sin, Firaministan ya ce kasar za ta iya jure matsi kan tattalin arzikinta da kuma dorewar muhimman tubalin tattalin arzki cikin lokaci mai tsawo, ta hanyar karfafa abubuwan dake bunkasa kasuwanni da bunkasa tunanin jama'a.

Ya ce bunkasa sana'o'i da kirkire-kirkire na samar da goyon baya mai karfi ga samar da aikin yi, yana mai cewa shirin ya samar da guraben ayyukan yi da dama ga Sinawa, musammam matasa.

Har ila yau, ya ce ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai su zurfafa gyare-gyare da ba da iko ga matakai na kasa da su, da inganta hidimomi da daidaita ayyuka, sannan dole ne su inganta yanayin kasuwanci da kara aiwatar da matakan rage haraji. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China