Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Libya na son fadada hadin-gwiwa da kasar Sin
2019-06-26 13:46:14        cri

Ministan harkokin wajen gwamnatin hadin-kai ta Libya Mohamed Taha Siala ya bayyana jiya Talata a Beijing cewa, yana matukar fatan karfafa hadin-gwiwa da kasar Sin don inganta tsaro da zaman lafiya, a wani kokari na aza tubali mai inganci ga hadin-gwiwar Sin da Libya har ma da dukkan kasashen Afirka baki daya.

Bayan da ya halarci taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC jiya Talata a Beijing, Mohamed Taha Siala ya bayyana cewa, kasarsa wato Libya na goyon-bayan wasu manyan matakai takwas da shugaba Xi Jinping ya bullo da su a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, yana kuma fatan Libya za ta karfafa hadin-gwiwa da Sin a fannonin da suka shafi murkushe ayyukan ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinsu.

Har wa yau, Mohamed Taha Siala ya ce, Libya na nuna himma da kwazo wajen shiga cikin ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", inda ya jaddada cewa, kasarsa na son taka rawar gani wajen inganta hadin-gwiwa da mu'amala da kasar Sin a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China