Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin soja na wucin gadi na Sudan ya yi alkawarin bin yarjejeniyar da ta cimma da 'yan adawa
2019-07-07 17:02:39        cri
Jiya kwamitin soja na wucin gadi na kasar Sudan ya bayyana cewa, zai bi yarjejeniyar da aka cimma tare da kungiyar Freedom and Change Alliance wato babbar kungiyar hamayya a 'yan kwanakin da suka gabata, game da kafa hukumar gudanarwa a lokacin wucin gadi ta kasar.

Shugaban kwamitin Abdel Fattah al-Burhan ya bada jawabi a gidan talibijin na kasar Sudan a wannan rana, inda ya ce, babu wanda ya sha kaye a cikin yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kwamitinsa da kungiyar Freedom and Change Alliance, kwamitin zai bi yarjejeniyar, tare kuma da bada tabbaci wajen gudanar da yarjejeniyar. Baya ga haka, ya sake nanata cewa, wannan yarjejeniyar za ta taimaka wajen tabbatar da zaman karko da ci gaba, da yaki da cin hanci da rashawa da kuma kafa wata kasa mai martaba da bin doka da oda.

A ranar 11 ga watan Afrilun bana, ministan tsaron kasar Sudan Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf, ya sanar da hambarar da mulkin Omar al-Bashir, tare kuma da kafa kwamitin soja na wucin gadi, don kula da harkokin kasar. A ranar 12 ga watan Afrilu, Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kwamitin rikon kwaryar, kana laftana-janar Abdel Fattah al-Burhan ya kama aikin nan take. A ranar 5 ga wannan wata kuma, kwamitin soja na wucin gadi da kungiyar Freedom and Change Alliance sun cimma yarjejeniya kan kafa hukumar gudanarwa ta wucin gadi. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China