Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta dogaro da kwarewa da kokarin da take yi wajen samun ci gaba
2019-07-24 20:18:59        cri

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya yi ikararin a kwanan baya cewa, wai barazanar bayanan sirri da Sin ke yi wa Amurka, ya fi na sauran kasashe tsanani. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba cewa, Sin ba ta sata ba kuma ba ta kwace ba, kana ba ta taba yin karya ba. Ta samu dukkan ci gaba ne bisa kwarewarta da kuma kokarin da al'ummarta take yi.

Bugu da kari, Madam Hua ta bayyana yayin da take amsa tambayar da aka gabatar mata game da rahoton da asusun IMF ta bayar, ta ce, kasashen duniya suka cimma matsaya daya cewa, Sin ta samu bunkasuwa ba tare da tangarda ba, kuma Sin za ta ci gaba da ba da gudunmawa wajen hanzarta bunkasar tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China