Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Angola sun amince su karfafa dangantakar dake tsakaninsu
2019-07-24 10:37:58        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Angola, Manuel Domingos Augusto, a jiya Talata, inda jami'an suka nanata aniyar cigaba da bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta aiwatar da batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya kansu, da karfafa matakan tuntubar juna da gwamnatin Angola. Ya bukaci bangarorin biyu su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu karkashin shawarar ziri daya da hanya daya da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika. Ya kara da cewa, bangaren kasar Sin zai cigaba da bada gwarin gwiwa ga kamfanonin kasar Sin da hukumomin kudaden kasar dasu kara zurfafa yin mu'amala da kasar Angola, da samar da tallafi ga kasar gwargwadon hali da kuma taimakawa kasar wajen fadada hanyoyin cigaban tattalin arzikinta.

Augusto, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Sin a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Angola, Joao Lourenco, ya yabawa taimakon da kasar Sin ke baiwa kasarsa na dogon lokaci, matakin da a cewarsa yayi matukar tasiri wajen bunkasa cigaban kasar ta Angola, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta cigaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China