Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da takardar bayanai game da batun tsaron kasa a sabon zamani
2019-07-24 11:26:44        cri

A yau Laraba gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayanai game da manufarta ta tsaron kasa a sabon zamanin da muke ciki kana da yin bayani game da hakikanin matakanta, da manufofin shirin, da kuma muhimmancin kokarin da kasar Sin ke yi na kafa ingantaccen tsarin tsaron kasa da rundunar soji mai karfi.

Ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya fitar da takardar bayanan Takardar bayanan mai taken "Tsaron kasar Sin a sabon zamani," da nufin kara fahimtar da al'ummar kasa da kasa kan tsarin tsaron kasar Sin.

Babban abin da takardar bayanan ta kunsa sun kasu kashi shida: yanayin da tsaron kasa da kasa ke ciki, manufar tsaron kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, sauke nauyin dake rataye a wuyan dakarun tsaron kasar Sin a sabon zamani, gyare-gyaren tsaron kasar Sin da harkokinta na soji, kudaden da suka cancanci fannin tsaro, da kuma gudunmowar da za'a bayar wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China