Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya zama tilas Sin za ta kasance dinkakkiyar kasa a duniya
2019-07-24 15:27:32        cri

A Laraba ne aka gabatar da takardar bayani game da aikin tsaron kasar Sin a sabon zamani, inda aka bayyana cewa, daidaita batun yankin Taiwan, da tabbatar da dinkuwar kasar, muradu ne masu tushe ga al'ummar Sinawa, kuma bukata ce da ta zama wajibi wajen farfado da al'ummar Sinawa. Kuma ko shakka babu, Sin za ta samun dinkuwarta.

Takardar ta nuna cewa, Sin na da niyya da kuma kwarewa wajen kiyaye ikon mulkinta da cikakken yankinta. Kaza lika ba ta yarda ko wane mutum, ko kungiya, ko jam'iyya, su kawo baraka ga kasar a ko wane lokaci, bisa ko wane irin mataki ba.

Idan an yi yunkurin hakan, rundunar sojojin kasar Sin za ta dauki matakan da suka wajaba bisa iyakacin kokarin ta, da nufin kare dinkuwar kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China