Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayanai: Kasar Sin ba zata taba neman yin kama karya ba
2019-07-24 13:58:25        cri

Kasar Sin ba zata taba neman yin mulkin kama karya, ko kuma yin shisshigi kan harkokin wata kasa a duniya ba, wannan na daga cikin kalaman da majalisar gudanarwar kasar Sin ta ayyana a cikin takardar bayanan da majalisar ta fitar a yau Laraba.

Takardar bayanan mai taken "Tsaron kasar Sin a sabon zamani" ta bayyana wannan jigo a matsayin sigar tsaron kasar Sin.

Tarihi ya tabbatar kuma zai cigaba da bayyana cewa kasar Sin ba zata taba bin irin salon da kasashen duniya masu karfin fada aji suka bi ba na neman yin babakere. Duk irin girman cigaban da kasar Sin ta samu, kasar Sin ba zata taba yiwa wata kasa a duniya barazana ko kuma neman yin katsalandan kan harkokin wata kasa ba, kamar yadda takardar bayanan ta ayyana.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China