Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani: Sin na nacewa manufar tsaron kasa
2019-07-24 11:24:56        cri

Wata takardar bayani da ofishin watsa labarai a majalissar zartaswar kasar Sin ya fitar, ta ce kasar Sin na nacewa manufar kare kai karkashin kudurorin ta na tsaron kasa a sabon zamani da ake ciki.

Takardar da aka fitar a jiya Talata, ta nuna cewa, Sin na bin salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin, matakin da ke kunshe da dabarun samar da ci gaba cikin lumana, da manufofin cudanyar kasa da kasa masu zaman kan su, da al'adun gargajiya mafi nagarta dake la'akari da zaman lafiya da lumana a matsayin jigo.

Kaza lika takardar ya jaddada kudurin kasar Sin, na aiwatarwa da manufofin tsaro a sabon zamani, dake da nufin kare 'yancin mulkin kai, da tsaro da ci gaban al'umma. Kaza lika Sin ba ta taba burin babakere, ko fadada tasirin ta a wasu sassa ba, wanda hakan shi ma jigo ne na manufofin kasar game da ayyukan soji a sabon zamani da ake ciki.

Daga karshe takardar bayanin ta ce, burin Sin a fannin tsaron kasa shi ne ci gaba da karfafa tsarin aikin sojoji bisa salon kasar, da mayar da rundunar mai kyakkyawan tasiri a matakin kasa da kasa, a fannin gina al'ummu masu makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China