Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin bata fuskancin janyewar kamfanoni masu yawa ba
2019-07-24 14:11:58        cri

Ma'aikatar harkokin masana'antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin ta bayyana cewa kasar bata fuskanci janyewar masana'antu na a zo a gani ba, kuma janyewar wasu masana'antu daga kasar ba wani bakon al'amari ba ne a tsarin gudanar da harkokin cinikayya na yau da kullum.

Mataimakin ministan harkokin masana'antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin, Xin Guobin, ya bayyanawa manema labaru cewa, tabbataccen al'amari ne a samu sauyawar jarin wasu kamfanonin zuwa yankuna mafiya araha, kuma sauya wuraren aikin wasu masana'antu ba wani al'amarin ba ne da zai iya shafar cigaban fannin masana'antu kasar Sin.

Jami'in yayi wannan tsokaci ne game da batun sauya shekar da wasu kamfanonin kasashen waje suka yi daga kasar Sin zuwa wasu makwabtan kasashe.

Xin Guobin yace, bisa la'akari da yawan kasuwannin cikin gida da take dasu, da cikakken tsarin masana'antu, da ingantattun kayayyakin more rayuwa, da kuma sabbin fasahohin zamani, har yanzu kasar Sin tana daya daga cikin muhimman wurare mafiya janyo hankalin masu zuba jari a fadin duniya, jami'in ya bayyana yadda tsarin zuba jarin waje a fannin masana'atun kasar Sin ke gudana.

A cewarsa, a shekarar 2018, fannin ya samu karin kashi 23 bisa 100 na jarin kasashen waje idan an kwatanta da yadda jarin da kasa da kasa ke zubawa a fadin duniya ke raguwa , ya kara da cewa, manyan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin sun yi amfani da kashi 13.4 bisa 100 na jarin da aka zuba tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China