![]() |
|
2019-07-23 20:20:12 cri |
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar da "Takardar bayani kan batutuwan tarihi dake shafar tarihin jihar Xinjiang" a jiya Litinin, inda ya musanta korafin da masu adawa da kasar Sin a ciki da waje suka yi, wanda ya gurbata tarihi da jirkita gaskiya da karya. Masanan kasashe daban-daban ciki hadda ferfesa a jami'ar koyar da harsuna na kasar Uzbekistan Tursunali Kuzyev da masanin kasar Rasha Oleg Yakovlev da sauransu sun nuna cewa, Xinjiang yankin kasar Sin ne da ba za a iya ware shi ba, kuma ya ci gajiya sosai daga manufofin kasar Sin, yana ci gaba da bunkasa da samun makoma mai kyau. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China