Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta yarda da duk wani shisshigin da kasashen waje kan batun Xinjiang ba
2019-07-11 20:32:16        cri
Wasu kasashe sun gabatarwa kwamitin kare hakkokin dan Adam na Majalisar Dinkin duniya sako, inda suka zargi gwamnatin kasar Sin dangane da manufofinta kan jihar Xinjiang. Game da haka, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, gwamnati gami da al'ummar kasar Sin suna da ikon yin magana kan batun da ya shafi Xinjiang, kana ba za su amince da duk wani katsalandan da kasashen waje suka yi kan batun ba.

Geng ya ce, akwai wasu kasashe wadanda suka danne gaskiya tare da shafawa gwamnatin kasar Sin kashin kaji, kana sun yi kokarin saka batun siyasa a cikin batun kare hakkin dan Adam, da yin shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasar.

Geng ya kara da cewa, hukumar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin na daukar wasu matakai ciki hadda kafa cibiyar karo ilimi da samar da horo don inganta yanayin tsaro a jihar domin shawo kan barazanar ta'addanci da masu nuna tsattsauran ra'ayi. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China