Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Horgos a jihar Xinjiang ya samu karuwar kudin shiga daga bangaren yawon bude ido
2019-07-05 10:41:06        cri

Birnin Horgos na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, ya samu kudin shigar da ya kai sama da yuan biliyan 5, kwatankwacin dala miliyan 727.6, daga bangaren yawon bude ido a cikin rabin farko na bana, adadin da ya karu da kaso 79.8 akan na bara.

Mataimakin shugaban hukumar kula da al'adu da yawon bude ido na birnin Horgos Ma Huanhuan, ya ce birnin zai samar da wurin yawon bude ido dake kan iyakar kasa da kasa, da shagunan sayar da kayayyakin da b asa bukatar a biya musu haraji, wadanda za su samu goyon bayan cibiyar kula da iyaka ta kasa da kasa ta birnin.

Cibiyar ita ce yankin cinikayya mara shinge na farko a duniya dake kan iyakar kasa da kasa, wadda ke da sama da shaguna 5,000 dake sayar da kayayyaki daga fadin duniya, da suka hada da abinci da kayan kwalliya da agogo da sauransu.

Horgos ya taba kasancewa hanya mai hada-hadar 'yan kasuwa dake bulaguro kan tsohuwar hanyar siliki. Kuma shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da Sin ta gabatar, ta samar da sabon kuzari ga birnin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China