Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani:Yankin Xinjiang ya samu gagarumin ci gaba a fannonin raya jin dadin jama'a da kare hakkin dan-Adam
2019-07-03 16:57:14        cri
Shugaban makarantar koyar da aikin lauya karkashin jami'ar horas da malamai ta Xinjiang Chen Tong, ya bayyana cewa, yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, ya dora muhimmanci matuka ga batun kare 'yancin kananan kabilu, har ma ya samu gagarumar nasara a fannonin raya jin dadin jama'a da kare hakkin dan-Adam.

Chen Tong ya bayyana hakan ne a gyefen taron kare hakkin kananan kabilun na kasar Sin karo 41 na hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD.

Jami'in ya shaidawa mahalarta taron da kungiyar dake nazarin harkokin kare hakkin dan-Adam ta kasar Sin ta shirya cewa, sama da kaso 60 cikin 100 na wakilan majalisar wakilan jama'a daga yankin Xinjiang kananan kabilu ne.

Ya ce, daga shekarar 1978 zuwa shekrarar 2016, GDPn yankin Xinjiang ya karu daga Yuan 313 kwatankwacin dalar Amurka 46 zuwa Yuan 40,427, kwatankwacin dalar Amurka 5,882, adadin da ya ninka sau 128.2.

Kana ya zuwa karshen shekarar 2016, yankin na da cibiyoyin kula da lafiya 15,721 da likitoci 51,000 fiye da matsakaicin adadi na kasa. Yana mai cewa, kowa ne musalmai 530 na da a kalla masallaci guda, matakin da ya biya bukatun yin addini na mazauna yankin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China