Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gabatar da takardar bayani kan batutuwan dake shafar tarihin jihar Xinjiang
2019-07-21 16:15:49        cri

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da takardar bayani kan batutuwan dake shafar tarihin jihar Xinjiang a yau Lahadi.

Takardar ta nuna cewa, Sin dinkuwar kasa ce dake da kananan kabilu da dama, jama'ar Xinjiang na da asili daya da al'ummar Sinawa. Makomar jihar tana da alaka matuka da makomar al'ummar Sinawa a cikin dogon tarihi. Duk da haka, masu nuna kiyayya a cikin gida ko a ketare musamman ma 'yan aware, masu tsattsauran ra'ayi ta fuskar addini, 'yan ta'adda sun jirkita gaskiyar tarihin don cimma mummunan burinsu na kawo baraka ga kasar Sin. Suna musanta abin da yake na gaskiya cewa, Xinjiang ba wata jihar kasar Sin ba ce, kuma Xinjiang ba wata jihar dake da al'umomi masu bin addinai daban-daban da mabambanta al'adu daban-daban ba ne, har sun yi ikirarin cewa, Xinjiang ita ce Sherqiy Türkistan suna kokarin ware jihar Xinjiang daga kasar Sin.

Takardar ta jaddada cewa, ba wanda zai iya yin zamba kan tarihi ko kadan, kuma ba wanda zai iya musanta gaskiya. Xinjiang wani kashi ne na kasar Sin, babu Sherqiy Türkistan, kabilar Uyghur ta kafu ne bisa kaurowar da aka yi da haduwar al'umomi daban-daban a cikin dogon tarihi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China