Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan jaridu daga kasashe 24 sun ziyarci Xinjiang
2019-07-23 20:03:58        cri

Wani rukunin 'yan jaridu daga kasashe 24 sun ziyarci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin daga ranar 14 zuwa 22 ga watan Yulin wannan shekara bisa gayyatar ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin.

A yayin rangadin, 'yan jaridun da suka fito daga kasashen Sin da Amurka, da Rasha da Italiya, da Japan da Saudi Arabiya da Turkiya da Iran, sun yi mu'amula sosai da manoman yankin, da dalibai da malamu da ma'aikata da kuma masu samun horo a cibiyoyin koyon sana'o'i dake yankin.

A jawabansu, 'yan jaridun sun yarda cewa, gwamnatin kasar Sin ta samu ci gaba a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci bisa doka, da kare 'yancin bin addini na al'ummarta, da kiyaye al'adun al'ummomin kananan kabilu da ma inganta rayuwar mazauna yankin baki daya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China