Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta samu ci gaba a fannin samar da makamashi mai tsafta
2019-06-26 17:01:19        cri
Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta samu ci gaba a fannin samar da makamashi daga hasken rana da iska, a cikin watanni hudun farkon shekarar nan, yayin da ake tsaka da kokarin inganta samarwa da amfani da makamashi mai tsafta.

Aikin samar da lantarki daga karfin iska a tsakanin wadancan watannin ya kai kwh biliyan 12.13, wanda ya karu da kaso 12.1, yayin da na hasken rana ya kai kwh biliyan 3.74, adadin da ya karu da kaso 12.7.

Domin rage fitar da gurbatacciyar iska, kasar Sin na ta kokarin kara amfani da makamashi mai tsafta domin rage dogaro akan makamashin kwal. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China