Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani game da yankin Xinjiang ta yi bayanai masu maana in ji wani masani
2019-07-23 10:57:44        cri

Wani kwararre game da harkokin kasar Sin dan asalin kasar Saudiyya mai suna Abdulaziz Alshaabani, ya ce takardar bayani game da yankin Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kansa da Sin ta fitar a ranar Lahadi, ta yi bayanai masu gamsarwa, tare da kawar da rashin fahimta, da zarge-zarge da wasu kafafen yada labarai ke yayatawa kan kasar Sin game da yankin.

Ya ce takardar mai taken "al'amuran tarihi masu nasaba da Xinjiang," ta tabbatar da cewa, yankin Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, tun fil Azal bangare ne na kasar da ba za a iya ware shi ba, kuma bai taba kasancewa yankin gabashin Turkistan ba.

Kaza lika Abdulaziz Alshaabani, ya ce tun da can, mabiya addinai daban daban sun rayu a wannan yanki cikin lumana, kuma addinin Islama bai taba kasancewa daya tilo, ko na asali ga al'ummar yankin baki daya ba.

Daga nan sai ya jinjinawa kwazon mahukuntan kasar Sin, game da aiwatar da matakan bunkasa tattalin arziki, da wanzar da kyakkyawan yanayin zamantakewar al'umma a Xinjiang, bisa hali da yankin ke ciki, wanda ya dace daukacin kasashen duniya su fahimta kuma su martaba.

Ya ce matakan da ake dauka a yankin, sun taimaka matuka wajen dakile yaduwar tsattsauran ra'ayi da ayyukan ta'adanci, sun kuma habaka ci gaba da zaman lumana a Xinjiang.

Shi ma a nasa tsokaci, shaihun malami a jami'ar Ain Shams dake kasar Masar Nasser Abdel-Aal, wanda kuma ya taba ziyartar yankin na Xinjiang, ya ce an sanya yankin Xinjiang a hukumance cikin babban yankin kasar Sin ne tun lokacin daular Han, wanda tuni abubuwan tarihi dake wannan yanki suka tabbatar da hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China