Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashen waje sun yaba da nasarorin da Xinjiang ta samu a fannin yaki da ta'addanci
2019-07-04 14:02:12        cri
Tawagar dindindin ta kasar Sin dake Geneva ta kira wani taro kan nasarorin da jihar Xinjiang ta samu a fannin kare hakkin dan Adam, inda ta gayyaci wakilai daga jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin da suka halarci taron kare hakkin dan Adam na MDD da wasu jakadun kasashen wajen da suka ziyarci Xinjiang a kwanakin baya don su bayyana halin da ake ciki yanzu a yankin na Xinjiang.

Jakadun kasashen waje sun yaba da babbar nasarar da yankin na Xinjiang ya samu wajen neman ci gaba da kare hakkin dan Adam gami da kawar da masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda.

A jawabin da ya gabatar jakadan kasar Sin dake Geneva Chen Xu ya bayyana cewa, gwamnatin Xinjiang ta dauki batun kare muradun kananan kabilu daban-daban da muhimmanci da daukar tsauraran matakan dakile 'yan ta'adda. A shekaru ukun da suka wuce, ba'a samu barkewar wani aikin ta'addanci ko daya ba a Xinjiang.

A jawaban da suka gabatar yayin taron, jami'an diflomasiyyar kasashen Najeriya da Koriya ta Arewa da Rasha da Eritrea da Somaliya da Burundi da Togo sun jinjina ci gaban da jihar Xinjiang a shekarun baya, da dimbin nasarorin da ta samu a fannonin da suka shafi rage fatara da yaki da ta'addanci gami da kawar da masu tsattauran ra'ayi.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China