Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Libya ta kama kwale mai dauke da bakin haure ba bisa doka ba
2019-06-17 13:57:45        cri
Sojojin ruwan yaki na kasar Libya sun bayyana a jiya cewa, rundunar sojan kiyaye tsaron teku ta kasar Libya ta kama wani kwale mai dauke da bakin haure ba bisa doka ba 91 a tekun dake gabashin birnin Tripoli, ciki har da mata uku da kanana yara biyu. Dukkansu sun fito ne daga sauran kasashen Afirka, an kai su zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Tripoli bayan da aka bada jinya da samar da gudummawar jin kai gare su. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China