Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tsawaita wa'adin dokar ta baci a Masar
2019-07-22 10:34:52        cri

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ayyana tsawaita wa'adin dokar-ta-baci game da tsaro a kasarsa da karin watanni 3, matakin da zai fara aiki tun daga ranar 25 ga watan Yulin nan.

Bisa tanajin dokar, sojoji da 'yan sanda za su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin dakile ayyukan ta'addanci, da datse hanyoyinsu na samun kudade. Kaza lika za su gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a dukkanin sassan kasar, da ba da kariya ga rayukan al'ummar kasar, da dukiyoyin gwamnati da na sassa masu zaman kansu.

Kundin tsarin mulkin kasar Masar dai ya baiwa majalissar dokokin kasar ikon dubawa, tare da amincewa da kudurin na shugaban kasa game da sabunta wa'adin dokar-ta-bacin. Yanzu dai sai majalissar wakilan kasar ta amince da wannan kuduri, kafin fara aiwatar da shi, kamar dai yadda sashe na 4 na kundin mulkin kasar ya tanada.

A karon farko, shugaban kasar ya kaddamar da dokar-ta-baci game da tsaro ta watanni 3 ne, a ranar 27 ga watan Afirilun shekarar 2017, biyowa bayan tagwayen hare-haren bama-bamai na kunar bakin wake da aka kaddamar a wasu majami'u biyu, dake lardin Gharbiya dake arewacin kasar, da kuma birnin Alexandria, lamarin da ya hallaka akalla mutane 47, tare da jikkata mutum sama da 120. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China