Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar na fatan kungiyar sada zumuncin Sin da Masar za ta ci gaba da ba da gudunmawarta a nan gaba
2019-07-21 16:22:12        cri

 

 

Kungiyar sada zumuncin Sin da Masar ta shirya wata liyafa a daren jiya Asaba a Alkahira, fadar mulkin Masar, don maraba da zuwan sabon jakadan Sin dake kasar Liao Liqiang. A cikin jawabinsa, jakada Liao ya nuna godiya sosai ga kokarin da kungiyar ta dade take yi, na himmantuwa wajen hadin kan kasashen biyu a dukkan fannoni, kuma yana fatan kungiyar za ta ci gaba da taka rawa wajen ingiza zumuncin kasashen biyu.

Liao Liqiang ya ce, dangantaka da kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu ya shiga wani mataki mafiya kyau a tarihi karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping da takwaransa Abdel Fattah al Sisi, dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu na zama abu mai muhimmanci kuma abin koyi ga sauran kasashe.

Mataimakin shugaban kungiyar Ahmed Waly, ya ba da jawabi cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta zama wani sabon zarafi ne ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, yana fatan kasar Sin ta kara hadin kai da Masar bisa tushen neman amfanawa juna da cin moriya tare, a fannin ciniki da tattalin arziki, zuba jari, yawon shakatawa da sauransu. Kungiyar za ta ci gaba da taka rawarta don kokarin ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China