Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya dandalin tattauna ci gaban aladun duniya a Masar
2019-06-10 11:59:03        cri

An kaddamar da dandalin tattaunawa kan ci gaban al'adun kasa da kasa karo na 7 wanda kasashen Sin da Masar suka shirya tare a jiya Lahadi a birnin Alkahira. Dandalin, mai taken "cimma ra'ayi daya da gina ra'ayin bil'adama na bai daya" an tattauna kan yadda za'a iya tinkarar ra'ayin nuna bangaranci, da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

Jami'ar Hubei ta kasar Sin ce ta ba da shawarar kafa wannan dandali wato dandalin tattaunawa kan ci gaban al'adun kasa da kasa, da nufin gudanar da shawarwari tsakanin kasar Sin da kasashen duniya ta fannin raya al'adu, da inganta mu'amala da cudanya tsakanin al'adu daban-daban. Wasu shahararrun jami'o'in kasar Sin, ciki har da jami'ar Hubei da jami'ar Zhongshan da jami'ar Tsinghua gami da jami'ar Ain Shams ta kasar Masar ne suka shirya dandalin tattaunawar a wannan karo cikin hadin-gwiwa.

A nasa bangaren, shugaban jami'ar Ain Shams ta Masar, Abd El Wahab Ezzat ya gabatar da jawabi, a cewarsa dandalin ya samar da wani sabon zarafi ga ci gaban al'adun kasashe da yankuna daban-daban, ta yadda jama'a za su iya yin shawarwari da kara samun fahimtar juna.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China