Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kera motoci na Sin da Masar sun kulla hadin gwiwa don kera motoci samfurin MG a Masar
2019-06-18 09:30:26        cri

Kamfanin kera motoci na SAIC na kasar Sin, da rukunin kamfanin sayar da motoci na Mansour dake Masar, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa jiya Litinin a birnin Cairo, domin kera motoci samafurin MG a Masar.

Da yake jawabi yayin rattaba hannun, shugaban kamfanin SAIC Chen Hong, ya ce kamfaninsa ya kafa sana'ar samar da motoci da ya kunshi bincike, da bunkasawa, da kerawa, da tallatawa, da samar da kayayyaki, da kudi a kasuwar duniya.

Ya ce a wannan lokacin, sun hada hannu da kamfanin Mansour. Yana mai cewa za a gabatar da sabbin kayayyaki, da fasahohi, da dabarun kamfanin SAIC ga kasuwar Masar, domin samarwa mutanen kasar karin kayyayaki da hidimomi masu inganci sosai.

Babban mai kula da ayyuka na kamfanin Mansour na kasar Masar, Ankush Arora, ya ce za a fara kera motocin ne bayan watanni 12 masu zuwa, yana mai cewa a yanzu haka, suna kafa kayayyakin harhada motoci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China