Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya taron dandalin tattaunawa kan yaki da cin hanci a Afirka karo na farko a Masar
2019-06-13 10:53:04        cri

Jiya Laraba ne aka bude taron dandalin tattaunawa kan yaki da cin hanci a Afirka karo na farko a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, inda manyan jami'ai da wakilai daga kasashe 50 na Afirka da kungiyoyin kasa da kasa 9 suka halara.

A cikin jawabinsa a yayin bikin bude taron, shugaba Abdel Fattah al Sisi na Masar ya ce, cin hanci yana hana bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka. Kamata ya yi kasashen nahiyar su hada hannu wajen kara karfin yaki da cin hanci ta hanyoyin kafa doka, aiwatar da doka, sa ido da dai sauransu.

A matsayinsa na shugaban kungiyar Tarayyar Afirka a wannan karo, shugaban Masar ya jaddada cewa, dole ne kasashen Afirka su karfafa aniyarsu ta yaki da cin hanci, su kafa tsarin taimakawa juna ta fuskar yaki da cin hanci, da hana cin hanci a sassa daban daban cikin hadin gwiwa. Ya kara da cewa, a shekarun baya, kasarsa ta samu ci gaba wajen yaki da cin hanci ta mabambantan hanyoyi.

A yayin bikin bude taron, wasu jami'an kasashen Afirka sun gabatar da jawabai kan yadda za a inganta kula da jami'an gwamnati da kyautata gudanar da harkokin gwamnati ba tare da rufa-rufa ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China