Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron kasa da kasa kan BRI da sabbin dabaru karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika a birnin Cairo
2019-06-17 09:53:44        cri

An kaddamar da taron kasa da kasa kan Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), da sabbin dabaru karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika, jiya Lahadi a Cairo, babban birnin kasar Masar.

Cibiyar nazarin kawancen shawarar BRI ta Afrika da Jami'ar Ain Shams ta Masar ne suka karbi bakuncin taron na yini biyu da cibiyar nazarin harkokin Afrika ta jami'ar koyon harsunan waje ta Guandong ta kasar Sin da cibiyar bincike kan shawarar BRI ta Jami'ar Ain Shams ne suka shirya.

Taron ya samu mahalarta taron 80 ciki har da jami'an gwamnatoci da 'yan kasuwa da masana da malamai da masu bincike daga kasashen Nijeriya da Kenya da Kasar Sin da Masar.

Yayin taron, masana da malamai za su tattauna kan yadda za a inganta ayyukan masana'antu tsakanin Sin da Afrika da alakar tattalin arzikin Masar da dangantakar Sin da Afrika da hadin gwiwar Sin da Masar karkashin shawarar BRI.

Za kuma su tattauna kan raya masana'atu da raya ilimin sana'o'in hannu a kasashen Afrika da sabuwar hanyar hadin gwiwar karkashin shawarar BRI.

Shawarar BRI da kasar Sin ta gabatar a 2013, na nufin hanyar cinikin siliki ta kasa da hanyar cinikin siliki na cikin ruwa na karni na 21, wadda ke da nufin gina ciniki da hanyar da za ta hada Asiya da Turai da Afrika, a kan tsohuwar hanyar siliki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China