Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya gudanar da bikin azumi a Masar
2019-05-14 10:00:56        cri
Kamfanin CSCEC reshen Masar ya gudanar da wani bikin azumi a daren Lahadi 12 ga wata a wurin aikinsa dake yankin ciniki na tsakiyar sabuwar hedkwatar kasar.

Babban direktan kamfani a Masar Mista Chang Weicai ya shirya wannan biki, kuma ya jaddada muhimmancin mutunta addini da al'adun Musulmai. Kuma ya nemi a kara ba da tabbaci ga tsaro a aikin dake yankin ciniki na tsakiyar sabuwar hedkwatar kasar don tabbatar da gudanar da ayyuka lami lafiya a lokacin watan Ramadan.

An ce, kamfanin yana shirin gudanar da irin wadannan bukukuwa har guda 10 tare da ba da kyautukan azumi, kuma za a tura wakilai zuwa gidan marayu, inda za su yi bikin murnar karamar sallah da marayun tare, da zummar karfafa donkun zumunci tsakanin ma'aikatan Sin da na Masar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China