Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwan fashewa sun tarwatse kusa da motar masu yawon shakatawa ya raunata mutane 14 a Alkahira
2019-05-20 10:38:58        cri

Shafin intanet na Ahram ya wallafa labarin cewa, wasu abubuwan fashewa sun tarwatse a ranar Lahadi a kusa da wata motar masu yawon shakatawa a lambun shakatawa na Grand Egyptian Museum dake Alkahira, babban birnin kasar Masar, mutane 14 sun samu raunuka.

Sai dai kuma, hukumomin kasar Masar basu sanar da yawan mutanen da suka jikkata ba a sanadiyyar faruwar lamarin.

Gidan talabijin na kasar Nile TV ya sanar cewa, harin ya lalata tagogin wata karamar mota da kuma mota kirar bus, wacce ke dauke da masu yawon shakatawa 25 'yan kasar Afrika ta kudu.

Kasar Masar ta jima tana fama da yaki da ayyukan ta'addanci lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan jami'an 'yan sanda da sojoji tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yulin shekarar 2013 biyowa bayan zanga zangar da aka gudanar a fadin kasar don don mayar da martani kan boren mulkinsa na shekara guda kuma a halin yanzu an haramta ayyukan kungiyarsa ta Muslim Brotherhood a kasar.

Yawancin hare haren ta'addanci a Masar an fi kaisu ne kan jami'an 'yan sanda da sojoji a arewacin Sinai kafin daga bisani ya watsu zuwa sassan kasar da dama inda ake samun hare haren kan mabiya addinin

Kiristoci kifdawa 'yan tsiraru, lamarin da ya haddasa mutuwar gwamman mutane a kasar.

Kungiyar dake zamanta a Sinai mai biyayya ga kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayin addini ita ce ke daukar alhakin galibin hare haren da aka kaddamar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China