An bude taron dandalin hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya na kasashen Sin da Afrika a karon farko

An bude taron dandalin hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya na kasashen Sin da Afrika a karon farko a babban dakin taron kasa da kasa dake birnin Beijing. Manyan jami'an hukumomin tsaro na kasashen Sin da Afrika ne suka halarci taron. Manufar taron shine karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro musamman bisa halin da ake ciki na kalubalolin tsaro dake addabar sassa daban daban na duniya.