Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana: Za a amfana daga shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya"
2019-07-12 13:15:53        cri

A jiya Alhamis, an yi wani taron karawa juna sani dangane da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, inda masana na kasashen Sin da Amurka, suka ba da shawarwari kan yadda za a karfafa hadin gwiwa karkashin shawarar a nan gaba.

Bankin Duniya ya gabatar da wani rahoto a watan Yunin bana, inda ya nuna yabo kan shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, ya ce shawarar na da ma'anar musamman ga cinikin kasa da kasa, da kuma karuwar zuba jari a duniya.

Alkaluman da aka gabatar a cikin rahoton sun nuna cewa, yadda ake kokarin aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", ya sa cinikayyar kasa da kasa ta karu da kashi 6.2%, da karuwar tattalin arzikin kasashe mahalarta shawarar da ta kai kashi 9.7%, gami da karin kudin shiga ga mutanen duniya da ya kai kashi 2.9%.

Dangane da alkaluman, Madam Naima Green, kwararriya a fannin ilimin tattalin arziki ta jami'ar Harvard dake kasar Amurka, wadda ke ziyara a jami'ar Renmin ta kasar Sin a yanzu, ta gaya ma wakilinmu cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya tana da amfani ga kasar Sin, gami da sauran kasashen da suka shiga shawarar. A cewarta, "Yanzu ana gudanar da ayyuka karkashin shawarar, wadanda za su haifar da tasiri sosai ga al'ummu daban daban, saboda makasudin hadin gwiwar shi ne samun damar amfanar kowa, wato sanya jama'ar kasashe daban daban, gami da ita kanta kasar Sin samun alfanu. Wannan hadin gwiwa za ta biya bukatun kasashen masu tasowa, wadanda ba su da karfin raya kayayyakin more rayuwarsu da kansu."

A nasa bangare, mataimakin shugaban cibiyar nazarin manufofi karkashin hadaddiyar kungiyar nazarin Asiya ta kasar Amurka Daniel Russel, ya ce kamfanonin Amurka da yawa na da niyyar halartar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", cikinsu akwai kamfanonin gini, da na jigilar kaya, da wadanda ke samar da hidimomi, da kuma bankuna. Ya ce, "A ganina kamfanonin Amurka suna da sha'awa sosai kan hadin gwiwar da ake yi karkashin shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya", musamman ma a fannonin samar da kaya, da hidimomi, da hada-hadar kudi, saboda sun ga akwai damar samun riba. Sai dai sun tabbatar da niyyarsu ne bisa tsarin kasuwanci, ba a lura da manufar siyasa ba tukuna. Yanzu ko muna da damar sanya wadannan kamfanoni su halarci shawarar? Ko za a ba su damar samun bayanai, gami da karfin zuci da suke bukata domin su halarta? A gani na, yadda kasar Sin take kokarin samar da saukin shiga kasuwanninta ga kamfanonin ketare yana da ma'ana sosai. Idan mun duba abubuwan da suka abku a baya, za mu ga cewa, kamfanonin kasar Amurka su kan jagoranci gwamantin kasar wajen daukar wasu matakai."

Bayan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" wasu shekaru 6 da suka wuce, ana ta samun karin kasashen da suka fara halartar shawarar. A shekarar 2018, kamfanonin kasar Sin sun zuba kudin da ya zarce dalar Amurka biliyan 15.6 ga kasashe mahalarta shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", adadin da ya karu da kashi 9%, idan an kwatanta da na shekarar 2017. Sa'an nan an yi amfani da jirgin kasa wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasashen Turai da kasar Sin, wanda ya yi tafiya tsakanin bangarorin 2 har karo 12000, tare da jigilar kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 16.

A birnin Duisburg na kasar Jamus, an samar da guraben aikin yi guda 6000, wadanda suka shafi aikin kula da layin dogon da ya hada nahiyar Turai da kasar Sin. Sa'an nan a kasar Kenya, an kaddamar da layin dogon da ya hada Mombasa dake bakin teku, da Nairobi, hedkwatar kasar, lamarin da ya samar da sabbin guraben aikin yi kimanin dubu 50, gami da daukaka matsayin tattalin arzikin kasar da kashi 1.5%.

A nasa bangare, Jia Jinjing, mataimakin shugaban cibiyar nazarin hada-hadar kudi ta jami'ar Renmin ta kasar Sin, ya ce, yadda ake kokarin hada hanyoyi da layin dogo na kasashe daban daban, zai samar da damar musayar kayayyaki da al'adu tsakaninsu. Sa'an nan kasar Sin ta yi kokari sosai don cimma wannan buri. A cewarsa, "Alkaluman da aka gabatar a kwanakin baya sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da rancen kudi da ya kai dalar Amurka biliyan 5000 ga kasashe daban daban cikin shekaru 5 da suka wuce. Yawancinsu sun shafi rancen kudin da wasu manyan bankunan kasar Sin suka ba kamfanonin kasar Sin dake daukar nauyin aiwatar da ayyukan gini a kasashen da suka halarci shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya'. Wadannan kudade sun kai kashi 2 cikin kashi 3 na dukkan rancen kudin da ake bayarwa a duniya, domin gudanar da aikin raya kasa."

Sa'an nan sauran masana na kasashen Sin da Amurka da suka halarci taron na karawa juna sanin, dangane da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", sun ce ya kamata a karfafa aikin tantance ayyukan da ake da niyyar gudanar da su a nan gaba, domin karfafa gwiwar al'ummun da ayyukansu suka shafi hakan, abin da zai taimaka wajen janyo karin jari daga kasuwannin duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China