Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nahiyar Afrika za ta ci gajiya daga baje kolin cinikayya tsakaninta da Sin
2019-06-14 10:53:28        cri

Masana kasuwanci da harkokin raya tattalin arziki na kasar Zambia, sun lura da cewa, kasashen Afrika na da dimbin alfanun da za su samu a baje kolin cinikayya na farko na kasashen Sin da Afrika, wanda zai gudana a cikin watan nan a kasar Sin.

Masanan sun yabawa kasar Sin bisa kirkiro baje kolin, suna masu bukatar kasashen Afrika su bincika tare da amfana daga damarmakin cinikayya dake akwai a kasar Sin da sauran wurare da kuma karfafa zuba jari a nahiyar Afrika da ma kasar Sin.

Shugaban kungiyar raya bangarori masu zaman kansu na kasar Yusuf Dodia, ya ce za a samu alfanu idan aka lalubo damarmakin cinikayya da kasar Sin, ta hanyar halartar irin wannan baje koli da Sin kan shirya lokaci zuwa lokaci, domin zai karfafa huldar cinikayya tsakanin kasa da kasa, baya ga wasu abubuwa.

Yusuf Dodia ya ce baje kolin cinikayyar zai taimaka wajen mayar da hankali ga kirkiran sabbin kayayyaki da hidimomi.

A nasa bangaren, Misheck Mwanza, masani kan harkar tattalin arziki na kasar Zambia, ya ce baje kolin dama ce ga Zambia na gano masu shawarar zuba jari a bangaren kafa cibiyoyin masana'antu a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China